Jump to content

Operation Provide Promise

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentOperation Provide Promise
Irimilitary operation (en) Fassara
Ma’aikatan jirgin C-17 Globemaster III na Rundunar Sojin Sama ta Amurka a filin jirgin sama da ke Sarajevo, Bosnia da Herzegovina, a matsayin wani ɓangare na aikin.

Operation Provide Promise wani aikin agaji ne na jin kai a Bosnia da Herzegovina a lokacin yakin Yugoslav, daga ranar 2 ga watan Yuli a shekarar 1992 zuwa 9 ga watan Janairu a shekarar 1996, wanda hakan ya sanya shi zama aikin jigilar agajin jin ƙai mafi daɗewa a tarihi.

A ƙarshen aikin, jirage daga ƙasashe 21 sun gudanar da tashi da sauka sau 12,886 zuwa Sarajevo, inda suka kai tan 159,622 na abinci, magunguna da sauran kayayyakin agaji, tare da kwashe mutane sama da 1,300 da suka jikkata. Amurka ta gudanar da jigilar kayayyaki ta jiragen C-130 sau 3,951, C-141 sau 236, da C-17 sau 10 ta hanyar saukar da jiragen a filin jirgin sama, inda aka kai tan 62,801.5 na kayayyaki. Haka kuma, ta gudanar da jigilar kayayyaki ta hanyar jefawa daga jiragen C-130 sau 2,222.

An samu hare-hare da sauran abubuwan da suka kawo cikas har guda 260, ciki har da harbo wani jirgin Rundunar Sojin Sama ta Italiya a watan Satumban a shekarar 1992, wanda ya yi sanadin mutuwar dukkan ma’aikatan jirgin guda huɗu da ke cikinsa.

  • Siege na Sarajevo

Operation Provide Promise ba aikin agajin jin ƙai ba ne a farko; sai daga baya, lokacin da tashin hankali a yankunan da ke kusa ya ragu, aka fara gudanar da shi a matsayin aikin agaji. Daga nan aka sauya aikin zuwa rundunar haɗin gwiwa (Task Force) domin tallafa wa ayyukan. A ɓangaren Rundunar Sojin Sama, an gudanar da jigilar kayayyakin agaji ta hanyar jefawa daga jiragen sama, yayin da a ɓangaren Rundunar Soji, ƙungiyoyin tsaro da na kiwon lafiya suka tallafa wa dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya da aka tura a yankin.